Mr. Yang, ya ce akwai bukatar sassan biyu su kara azama wajen cin gajiya daga wannan dandali, su kuma fadada alakar su karkashin inuwar manufar hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa.
Jakadan na Sin wanda ya yi wannan tsokaci cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar Zambia Daily Mail, ya kara da cewa taron dandalin FOCAC na da dadadden tarihi, zai kuma zamo ginshikin habaka huldar sassan biyu. Kaza lika a cewar sa manufar hadin gwiwa ta tsakanin kasashe masu tasowa da Sin ke aiwatarwa, na kan sahun gaba wajen inganta huldar diflomasiyyar Sin da Afirka, a yunkurin ta na cimma kyakkyawar alaka da sauran kasashen duniya.
Sharhin ya kuma bayyana cewa mafiya yawan kasashe masu tasowa na nahiyar Afirka, kuma nahiyar tana da albarkatu, da ma'adanai masu tarin yawa, baya ga kasuwa da damammaki na samun bunkasa. Don haka ne ma kasar Sin ke fatan tallafawa nahiyar Afirka, a fagen cimma nasarar bunkasar tattalin arziki, da dogaro da kai, tare da samun ci gaba mai dorewa.(Saminu Alhassan)