in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 25 sun rasu sakamakon harin boma-bomai da aka tayar a Aden
2016-03-26 12:55:43 cri
Hukumomin tsaron kasar Yemen sun ba da labari cewa, an tayar da harin boma-bomai na kunar bakin wake a daren jiya ranar 25 ga wata, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla 25, yayin da raunatar wasu mutane.

Wani jami'in bangaren soja da nemi a sakaya sunan shi ya ce, an samu harin ne a unguwar da hedkwatar rundunar hadin kan sojoji na kasashe da dama take a Aden, rundunar dai na karkashin jagorancin kasar Saudiyya. Wannan jami'in ya kara da cewa, wani mutum ne ya tayar da bom a wata motar daukar marasa lafiya dake dab da wata tashar bincike, wadda ke iya zuwa muhimman sansanonin na kasashen Saudiya da Hadaddiyar daular Larabawa dake Aden. Kana kuma masu kunar bakin wake guda biyu sun tayar da bom a wata tashar bincike dake wani sansanin soja, sansanin dai sojojin na kasashen biyu daruruwa suke a nan.

Wani asibitin da gwamnati ke baiwa tallafi ya bayyana cewa, jerin boma-bomai da aka tayar sun haddasa rasuwar mutane a kalla 25, wadanda yawancinsu fararen hula ne, yayin da raunatar wasu 15.

Wani jami'in gwamnatin wurin ya ce, bayan aukuwar harin, masu kai farmaki fiye da goma sun yi nufin kai hari kan hedkwatar rundunar sojojin hadn gwiwar, amma ba su cimma burinsu ba sakamakon harbe da jiragen saman soja da jiragen sama masu saukar ungulu suka yi. A yanzu haka sojojin kasashen Saudiya da Hadaddiyar daular Larabawa suna kokarin kaman masu tayar da harin.

An ce, kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta IS ta amince da tayar da jerin boma-bomai a wannan rana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China