in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kashi 74 cikin 100 na mutanen Turai na bukatar karin matakai daga EU domin magance kwararar 'yan gudun hijira
2016-08-10 10:53:54 cri

Kimanin kashi 74 cikin 100 na al'ummar Turai na bukatar ganin kungiyar tarayyar Turai wato EU ta kara daukar matakai domin daidaita matsalar kwararar 'yan gudun hijira, a cewar wani binciken jin ra'ayin jama'a na Eurobarometer da majalisar Turai ta dauki nauyi.

A cewar sakamakon wannan bincike da aka fitar a ranar Talata kan shafin internet na majalisar Turai, kimanin kashi 2 cikin 3 na mutanen da aka ma tambayoyi na ganin cewa, matakan EU gaban matsalar 'yan gudan hijira ba su wadatu ba.

Wannan bincike na Eurobarometer an gudanar da shi kan mutane 27,969 na kungiyar EU, daga ranar 9 zuwa 18 ga watan Afrilu.

A cewar hukumar kan iyaka ta EU, Frontex, jimillar adadin bakin haure da suka ratsa kan iyakokin wajen tarayyar Turai da aka gano ta karo zuwa miliyan 1,83 a shekarar 2015, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Turai na fama da matsalar kwararar 'yan gudun hijira sosai, dubban mutane na ficewa daga kasashensu dalilin yake-yake da talauci inda suke ratsa kasashen Turai domin neman tsaro da rayuwa mai kyau. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China