in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar People Daily: Kara himmatuwa domin karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen tsakiya da na gabashin Turai
2016-06-17 14:16:28 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake kai ziyara a kasashen yankin tsakiya da na gabashin Turai wato Serbia da Poland bayan watanni uku kawai da ya kai ziyara a kasar Czech a karo na farko. A yau Jumma'a 17 ga wata, jaridar People Daily ta gabatar da wani sharhi mai suna "Kara himmatuwa domin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen tsakiya da na gabashin Turai, inda aka bayyana cewa, za a fara wata ziyara mai ma'ana sosai. Dangantaka tsakanin bangarorin biyu na bude wani sabon babi.

Sharhi ya ce, ko da yake akwai bambanci sosai tsakanin bangarorin biyu a fannonin tsarin zaman al'umma, da yanayin kasa, da al'adu da sauransu, amma sun sami babban sakamako ta hanyar amincewa da juna da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, zuba jari, manyan kayayyakin amfanin jama'a, hada hadar kudi, yawon shakatawa, tarbiya, aikin noma da dai sauraunsu, hakan ma ya kawo alheri ga jama'arsu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China