An gudanar da bikin bude cibiyar ce a cibiyar tarurruka ta Turai dake birnin Amsterdam na kasar Netherlands, kasar da ke shugabantar kungiyar EU a wannan karo. A jawabinsa babban darektan kungiyar 'yan sanda masu bincike laifuffuka ta Turai Rob Wainwright ya bayyana cewa, kasashen Turai suna fuskantar barazanar ta'addanci mafi tsanani a cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata, inda suke fuskantar barazanar yiwuwar kai musu hare-hare a nan gaba, don haka kafa cibiyar yaki da ta'addanci ta Turai muhimmin mataki ne ga kungiyar EU don mayar da martani ga duk wasu barazanar ta'addanci.
Mr Wainwright ya kara da cewa, kungiyar 'yan sanda masu bincike laifuffuka ta Turai tana fatan cibiyar za ta taimaka wajen samar da muhimman bayanai game da yaki da ta'addanci a EU, da ba da shawara ga binciken da ake yi, da gudummawa wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa idan hare-hare suka faru. Hakazalika ya jaddada cewa, kungiyar 'yan sanda masu bincike laifuffuka ta Turai ta tabbatar da cewa, za a adana dukkan muhimman bayanan tsaro da aka samu, kana ya yi kira ga kasashe membobin kungiyar EU da su yi imani da wannan cibiya. (Zainab)