A yayin taron, Li Keqiang ya ba da jawabi cewa, a halin yanzu, ana cikin yanayin zaman lafiya da zaman karko a galibin yankunan Asiya da na Turai, amma babu shakka, ana fuskantar wasu kalubaloli wajen tabbatar da tsaron yankunan, musamman ma game da babban kalubalen ta'addanci da ake fuskanta a halin yanzu, wanda ya kasance babban kalubale ga kasa da kasa.
Don gane haka, ya kamata kasashen duniya su yi hadin gwiwa wajen karfafa ayyukan yaki da ta'addanci, domin gina zaman takewar al'umma cikin lafiya yadda ya kamata, da kuma kawar da kalubalen gaba daya daga tushensa. (Maryam)