in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Zhaoxing ya gana da tsohon firaminista da tsohon shugaban kasar Tanzaniya
2016-08-09 20:14:42 cri

A jiya Litinin ne, shugaban kungiyar kula da harkokin diplomasiya ta Sin, Li Zhaoxing dake halartar dandalin tattaunawar harkokin diplomasiya tsakanin Sin da kasashen Afirka a kasar Tanzaniya ya gana da tsohon firaministan kasar, Salim Ahmed Salim, da kuma tsohon shugaban kasar, Benjamin Mkapa da ayarinsa.

Li ya bayyana cewa, karfafa hadin kai da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka muhimmin tushe ne a harkokin diplomasiyar Sin, kuma tsari ne da Sin ta dade tana gudanarwa. Li ya yabawa kasashen Afirka sosai, ciki har da Tanzaniya, game da yadda suka nuna goyon baya ga Sin kan batutuwan dake shafar babbar moriyarta. A kwanan baya, wasu kasashen Afirka sun sake fitowa fili suka bayyana goyon baya ga matsayin da Sin ke dauka kan batun tekun kudancin kasar da batun yin kwaskwarima ga kwamitin sulhun MDD. A saboda haka jama'ar Sin sun sake fahimtar irin dankon zumunci dake tsakaninsu da jama'ar kasashen Afirka, tare da nuna musu godiya.

A nasu bangare, Mr. Salim Ahmed Salim da Mr. Benjamin Mkapa sun bayyana cewa, tarihi ya bayyana cewa, ko da yake kasar Sin babbar kasa ce, amma ba ta taba nuna fifiko ga sauran kasashen duniya ba. Kasashen Sin da Tanzaniya sun kulla dankon zumunci a tsakaninsu ne bisa adalci da taimakawa da kuma girmamawa juna.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China