in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya: Cutar kwalara ta halaka mutane 320 daga watan Augustan shekarar 2015
2016-04-05 10:05:48 cri
Tun cikin watan Augustan shekarar 2015, cutar kwalara ko amai da gudawa ta shafi mutane fiye da dubu 20 a kasar Tanzaniya, inda daga cikinsu mutane 320 suka mutu, in ji ministar kiwon lafiya na Tanzaniya, madam Ummy Mwalimu a ranar Litinin.

Ta bayyana damuwarta bisa adadin da ke karuwa na masu kamuwa da cutar ta amai da gudawa, tare tabbatar da cewa wannan annoba ita ce mafi tsanani tun daga shekarar 1978. Gwamnatin kasar ta samu fadakar da jama'a kan matakan yaki da annobar, amma cigaba da aka samu ba mai gamsarwa ba ne, in ji madam Mwalimu a cikin wata sanarwa. Ruwan sama suna taimakawa sosai wajen bazuwar wannan cuta da ke da alaka da ruwa, ganin cewa ruwa mai tsafta da kuma kayayyakin kiwon lafiya sun kasance babu su sosai a cikin yawancin yankunan kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China