in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya da Uganda sun cimma matsaya guda game da warware rikicin iyakokin kasashen biyu
2016-04-11 13:19:55 cri
Kasashen Tanzaniya da Uganda sun cimma matsaya guda game da warware matsalolin dake shafar zaman rayuwar mutane a iyakokin kassahen biyu wadanda ke yankin gabashin nahiyar Afrika, ciki har da batun bakin baure da batun tsaro.

An daddale yarjejeniyar a yayin wani taron da aka gudanar a yankin Kagera dake yankin arewa maso yammacin kasar Tanzaniya mai nisan kilomita 298 daga birnin Kampala, hedkwatar kasar Uganda, inda manyan jami'ai da kwararru na kasashen biyu sula halarta.

Mataimakin zaunannen sakatare na ma'aikatar kula da yankuna da gidaje da raya matsugunan dan Adam na Tanzaniya Dr. Moses Kusiluka ya ce, wannan mataki zai kyautata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China