in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rukunin jiragen ruwan sojan ba da kariya na 22 na kasar Sin ya kai ziyara a kasar Tanzaniya
2016-05-31 11:11:51 cri

Rukunin jiragen ruwan sojan ba da kariya na 22 na kasar Sin ya isa tashar jirgin ruwa ta Dar es Salaam a jiya Litinin, domin fara ziyararsa ta tsawon kwanaki 4 a kasar Tanzaniya.

A wannan rana da karfe 9 na safe, a karkashin jagorancin manjo janar Chen Shaonan, jiragen ruwan sojan ba da kariya na kasar Sin sun shiga tashar Dar es Salaam. Sojojin Sin dake sanya tufafin soja masu launin fari sun rika daga hannaye domin nuna gaisuwa ga mutanen dake maraba da su.

Sojijin ruwa na kasar Tanzaniya sun yi bikin maraba da sojojin Sin a tashar. Kwamanda da sojojin ruwa na kasar Tamzaniya da jakadan kasar Sin dake kasar Tanzaniya Lv Youqing da kuma jami'an ofishin jakadanci da wakilan kamfannonin Sin da kuma Sinawan dake Tanzaniya sun yi maraba da zuwan sojojin ruwan Sin. Bayan da aka kammala bikin, wakilan sojojin ruwan kasar Tamzaniya da na kamfannonin Sin da Sinawa sun hau kan jiragen ruwan soja domin bude ido.

A lokacin ziyararsu, jami'an rukunin jiragen ruwan sojan ba da kariya na Sin za su kai ziyara a sansanin sojojin ruwa da jiragen ruwan soja na kasar Tanzaniya, kuma za su yi musayar ra'ayi tare da sojojin ruwan kasar Tanzaniya a fannoni daban daban.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China