in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya ta nuna goyon baya kan kasar Sin game da tekun kudancin Sin
2016-06-01 13:51:50 cri
A jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Tanzaniya Augustine Magiha ya bayyana a taron majalisar wakilan jama'ar kasarsa cewa, Tanzaniya tana goyon baya kasar Sin game da batun tekun kudancin kasar.

Magiha ya ce, game da batun ikon mulkin tekun kudancin kasar Sin, kasar Tanzaniya tana goyon baya matsayin kasar Sin, tana kuma fatan kasashen da batun ya shafa za su yi shawarwari don warware batun cikin ruwan sanyi, tare da bin ka'idojin dake kunshe cikin yarjejeniyar teku ta M.D.D. da aka tsara a shekarar 1982, don girmama mulkin kai, da ikon zabin hanyar warware rigingimu.

Magiha ya ce, yanzu haka ana fuskantar tafiyar hawainiya wajen raya tattalin arziki, tekun kudancin Sin ya zama wata cibiyar raya tattalin arziki da samar da kayayyaki, da yin cinikayya, Yayin da Tanzaniya ta yi imani cewa, hanya mai kyau wajen warware batun tekun kudancin Sin ita ce, ta yin shawarwari da kasashen da abun ya shafa.

Magiha ya jinjinawa taron koli na dandanlin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da aka yi a birnin Johannesburg, kana ya yaba wa matakan da Sin ta bayyana a yayin taron cewa, nan da shekaru 3 masu zuwa, za a gudanar da shirin hadin gwiwa a fannoni 10 da kafa asusun bunkasa hadin gwiwa a fannin samar da makamashi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China