Wannan haduwa ta kwanaki biyu wacce ta samu halartar masu fada a ji na kasashen shiyyar, ta taimaka wajen daukar matakai da kudurori domin cigaba da aiwatar da tsarin nuni na shiyyar (PIR) na asusun cigaba na kungiyar tarayyar Turai na goma (10e FED) da kuma shirye shiryen aiwatar da shirin FED na goma sha daya (11e FED).
Bisa la'akari kan cewa babu wani cigaba idan babu zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankalin shiyyar, EU ta nuna damuwa game da karuwar ayyukan ta'addanci a yammacin Afrika, musammun ma a kasashen Burkina Faso, Cote d'Ivoire, Nijar da Najeriya tare da bayyana goyon bayanta ga wadannan kasashe da matsalar ta shafa.
Haka kuma, kungiyar tarayyar Turai ta bayyana gamsuwarta kan cigaban da aka samu wajen tabbatar da zaman lafiya a shiyyar tare da jaddada niyyarta na yaki da wannan matsala da matakan da suka dace, yaki da wannan annoba dake kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron shiyyar da ma kasa da kasa. (Maman Ada)