in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da shugaban kasar Togo
2016-06-01 10:52:33 cri

A jiya ne firaministan Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Togo Faure Essozimna Gnassingbé wanda ke yin ziyarar aiki a nan kasar Sin a babban dakin taron jama'a da ke birnin Beijing.

A jawabinsa firaministan Li ya yi nuni da cewa, kasashen Sin da Togo na da dankon zumunci a tsakaninsu,kuma kasashen biyu suna amincewa juna a fannin siyasa, kuma hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu ta samu sabon ci gaba.

Ya kara da cewa, kasar Sin tana fatan bangarorin biyu za su yi amfani da fiffiko na kowanensu, su tashi tsaye wajen inganta hakikanin hadin gwiwa a tsakaninsu ta fannonin raya muhimman ababen more rayuwa, da gina tashoshin jiragen ruwa, da hako ma'adinai da sauransu, sa'an nan su sa himma wajen gina hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya, da hanyoyin mota, da na jiragen sama na shiyya-shiyya, don cimma burin samun bunkasuwa da nasarar juna.

A nasa jawabi shugaba Faure ya ce, kasashen Togo da Sin na da dankon zumunci, kuma kasar Sin ta gabatar da ra'ayin inganta hadin gwiwa a fannin gina hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya, da hanyoyin mota, da jiragen sama na shiyya-shiyya, da raya masana'antu, kuma an samu nasarori da dama. Kasar Togo tana fatan yin amfani da wannan babbar damar da ke kasancewa cikin tarihin dangantakar kasashe biyu, sa'an nan su yi amfani da fiffikonsu wajen kyautata yanayin kasuwanci, don inganta hadin gwiwa a fannin muhimman ababen more rayuwa da sufurin kayayyaki da hako ma'adinai, da rage talauci, a kokarin samun bunkasuwar kasar Sin da kasashen Afrika tare.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China