Sojojin biyar sun mutu a yayin wani kwanton bauna a Sevare dake kusa da birnin Mopti dake tsakiyar kasar Mali a lokacin da suke cikin wani rukunin zaratan sojojin sintiri da ba da tallafi da kuma rukunin dakaru na hudu. Wannan karramawar za ta kasance wata dama ga 'yan kasar Togo da su yi addu'o'i domin kwanciyar mamatan biyar dake aikin kare zaman lafiya.
Togo ta tura kusan sojoji dubu guda a kasar Mali a cikin tsarin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA), dake da sansaninsu a Douinza tare da wasu runkunoni a Gosso da Sevare. (Maman Ada)