in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Togo na fatan tattara Sefa biliyan 96 domin kiyaye gabar Lome da Cotonou
2016-06-25 12:51:20 cri
Kasar Togo na shirin tattara Sefa fiye da biliyan 96 daga wajen abokan huldarta domin sake farfado da hanyar Lome da Cotonou, tare da kiyaye gabar dake tsawon kan hanyar.

Faraministan Togo Selom Komi Klassou tare da rakiyar darektar yammacin Afrika da tsakiya a babbar cibiyar bunkasa cigaba da dangantaka ta kwamitin tarayyar Turai, madam Carla Montesi da wakilan kungiyoyin bada lamuni na kasar Togo, sun gudanar a ranar Jumma'a da wani rangadin gani da ido kan hanyar Baguida-Avepozo, dake bisa shirin sake farfado da hanyar Abidjan da Lagos, domin ganin halin da aka ciki musammun wadanda suke nasada da zaizayewar gabar Togo dake karuwa.

A cewar shirin zuba kudin, bankin BAD, tarayyar Turai (EU), bankin BEI, bankin BOAD, bankin zuba jari da cigaban ECOWAS (BIDC), asusun kiyaye muhalli na duniya (FEM), kungiyar UEMOA da gwamnatin Togo kowa ne daga cikinsu zai kawo gudummuwarsa domin hada Sefa biliyan 96.543.

Sai dai domin karfafa shirin kudin da za a zuba kan wannan aiki, gwamnatin Togo ta isar, cikin watan Nuwamban shekarar 2015, da wasu bukatunta ga EU da bankin BEI.

Faraministan Togo na bada muhimmanci sosai kan abubuwan da suka shafi kare muhalli na wannan shiri, tare da aza ayar tambayar cewa ina amfani sake farfado da wannan hanya idan ba'a warware matsalar zaizayewar gabar ba?

Ya bayyana cewa kare gabobin matsala ce da ta shafi hukumomin Togo sosai dake mayar da ita a matsayin wani babban mataki domin tabbatar da sake farfado da sabuwar hanyar tare da kare al'ummomin dake rayuwa a yankin daga matsowar teku. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China