in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar: an kaddamar da gangamin rigakafin zazzabin cizon sauro
2016-08-09 11:18:36 cri

Mahukunta a jamhuriyar Nijar sun kaddamar da shirin yin rigakafin zazzabin cizon sauro a tsakanin kananan yara, domin kare yara kanana 'yan watanni uku da haifuwa zuwa shekara biyar daga kamuwa da wannan ciwo cikin jahohi guda bakwai daga cikin jahohi guda takwas na kasar.

Mutane sama da 9000 ne za su tafiyar da wanna gangami da zai gudana cikin watanni 4, a ma'aikatun kiwon lafiya na gundumomi 27. Kazalika aikin zai kashe kudi har billion 4.5 na Sefa.

Manufar wannan gangami dai ita ce yi wa yara fiye da miliyan 2 'yan watanni 3 zuwa watanni 59 da haifuwa rigakafi a jahohin Zinder, da Maradi, da Tawa, da Dosso, da Yamai, da Difa da Tillabery.

Albarkacin gangamin za'a yi wa yaran rigakafin da zai ba su kariya daga zazzabin ciwon sauro, a lokacin da ciwon ya fi tsanani a kasar.

Bincike na ma'aikatar kididdiga ta kasar ya nuna cewa, zazzabin ciwon sauro ya yi sanadiyar rasuwar mutane sama da miliyan 2 wadanda aka tabbatar a shekara 2015, kuma kaso 60 da ke cikin 100 yara ne 'yan kasa da shekaru biyar. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China