Gwamnatin Nijar zata gina wani babban asibitin misali
Gwamnatin Nijar ta cimma a ranar Jumma'a, a zaman taron ministoci, da wani kudurin da ya shafi gina wani babban asibitin misali, wanda kasar Sin ta bayar da taimakon ginawa, da kuma za a shirya bikin bude shi nan bada jimawa ba a birnin Niamey. Fiye da kudin Sefa biliyan 40 suke shiga cikin wannan gini, dake da karfin daukar gadaje 500, kuma ginin, zai kasance babban asibiti mafi girma na zamani a matsayin wani misali a yammacin Afrika, a cewar hukumomin Nijar. Asibitin ya hada dukkan ayyukan likitanci ciki, musammun ma wuraren karbar majinyata cikin gaggawa, dakin binciken kwakwalwa, bangaren yin tiyata dake kunshe da dakuna shida, dakin gudanar da bincike, bankin ajiyar jini, radiyo da kuma jinya. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku