in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nijar sun kai wani babban samame kan Boko Haram har cikin Najeriya
2016-07-28 10:21:47 cri

Sojojin kasar Nijar na FDS sun kaddamar tun a ranar Litinin da ta gabata, su kadai, da wani babban samame kan kungiyar Boko Haram, har cikin makwabciyar kasar Najeriya, kamar yadda kafofin watsa labarai na kasar Nijar suka rawaito a ranar Laraba a birnin Niamey. A cewar yawancin wadannan kafofin, musammun ma gidan rediyo "Amfani" mai zaman kansa da kuma "Air Info", wani dogon ayarin tankokin yaki da manyan motocin yaki dauke da manyan makamai na sojojin FDS sun shiga a ranar Litinin, a jihar Diffa, gadar da ake kira "Doutsi", da tafkin "Komadougou Yobe", da ya kasance wata kan iyaka tsakanin Nijar da Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China