in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tallafa wa Nijar da kudaden aiwatar da wasu muhimman ayyuka
2016-08-02 20:44:29 cri

Gwamnatin kasar Sin ta tallafawa jamhuriyar Nijar da zunzurutun kudi har Yuan miliyan 300, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 45, kudaden da za a yi amfani da su wajen aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa.

Wata majiya daga gwamnatin kasar ta Sin ta bayyana cewa, tallafin ya biyo bayan rattaba hannu da aka yi ne, kan wata yarjejeniya tsakanin sassan biyu, a ranar 29 ga watan Yulin da ya gabata a nan birnin Beijing.

Wakiliyar jamhuriyar Nijar, kuma mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar El Back Zeinabou Bako, ita ce ta sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin kasarta, lokacin da take halartar taron masu sanya ido, wajen tabbatar da nasarar aiwatar da tsare-tsaren ci gaba da Sin ta gabatar, yayin taron dandalin Sin da Afirka na FOCAC, wanda ya gabata a bara a Afirka ta Kudu.

Cikin muhimman ayyukan da ake fatan aiwatarwa da kudaden, akwai kammala aikin Asibitin kwararru dake birnin Yamai, da ginin bangare na uku na gadar kogin Naija, da dai sauransu.

Sin da Nijar dai sun shafe tsawon lokaci suna raya huldar kawance tsakaninsu, a tsawon wannan lokaci ne kuma Sin ta zuba jari mai dimbin yawa, domin tallafawa Nijar din cimma nasarar raya sassa daban daban na tattalin arzikinta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China