in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayar da gudummawar abinci ga mutanen dake fama da cutar kanjamau a Nijar
2016-07-08 19:02:40 cri

Ofishin jakadancin kasar Sin da ke Jamhuriyar Nijar ya bayar da gudumawar kayayyakin abinci ga mutanen da ke fama da cutar kanjamau a kasar.

A lokacin da ya ke mika kayayyakin abinci a jiya Laraba, jakadan kasar Sin a Jamhuriyar Nijar Shi Hu ya ce, gudumawar wata sabuwar hanya ce ta inganta rayuwar mutanen da ke fama da wannan lalura.

Kayayyakin abincin da kasar din ta bayar sun hada da shimkafa,madara,garin filawa,man girki,wake da kifi da sauran kayayyaki. Ana kuma saran iyalai sama da 250 da suka hada da marayu da manya da matan da suka rasa mazajensu ne za su amfana da wadannan kayayyaki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China