Mambobi biyu na tawagar Nijar zasu halarci wasan ninkaya, wasu biyun su halarci wasannin guje guje da tsalle tsalle, guda a wasan Judo da kuma wani guda a wasan Taekwondo.
Shugaban Nijar ya mika tutar kasa ga Abdoulrazak Issoufou Alfaga, da dukkan 'yan Nijar suke alfahari da shi kan wadannan wasanni. Mai rike da damara baka a ajin dan na wasan Taekwondo, a yanzu haka yana na goma sha daya bisa jerin 'yan wasan Taekwaondo na duniya kana na biyu a Afrika.
Shugaban kasa ya bukace su da kadda suyi kasa a gwiwa ga fatan kasa baki daya, musammun ma idan aka yi la'akari da kudi da kayayyaki da aka sanya musu. Tawagar Nijar zata bar Niamey a ranar Litinin domin zuwa kasar Brazil.
Nijar na halartar wasannin Olympic karo na goma sha daya. Kuma kasar ta samu lambar yabo ta tagwulla har zuwa wannan lokaci tare da dan wasan dambe Issaka Dabore a wasannin Munich na shekarar 1972. (Maman Ada)