Wakilin kungiyar tarayyar Afirka wato AU a kasar Somalia Francisco Madeira, ya jaddada aniyar kungiyar AUn, ta aiki kafada da kafada da mahukuntan kasar, wajen tabbatar da cikakkiyar nasarar babban zaben kasar dake tafe.
Mr. Francisco Madeira, ya ce, tawagar AMISOM za ta yi duk mai yiwuwa, wajen ganin an kammala zaben kasar cikin yanayin zaman lafiya da lumana, musamman ta hanyar samar da tallafin kayan aiki, da managartan tsare-tsare, tare da tabbatar da cewa, sashen zartas da zaben kasar, ya yi aiki da dukkanin tanaje-tanaje da za su ba da damar gudanar zaben 'yan majalissun dokoki, da na shugaban kasa yadda ya kamata.
Madeira wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Litinin, ya kuma yi kira ga jama'ar kasar Somalia da su yi amfani da wannan dama, wajen shiga a dama da su a babban zaben kasar, wanda zai share fagen zabe na gaba da zai gudana a shekara ta 2020, lokacin da ake fatan aiwatar da zabe bisa tsarin mutum guda kuri'a guda.(Saminu)