Bam na farko ya fashe ne a kofar shiga filin jiragen saman, kana bam na biyu kuma ya fashe a kofar shiga sansanin tawagar musamman ta kungiyar AU dake kasar Somaliya dake dab da filin jiragen saman.
Kakakin tawagar musamman ta AU dake kasar Somaliya ya bayyana cewa, an kai harin kan sansanin dake dab da filin jiragen saman, kana yana kusa da sansanin MDD da wasu ofisoshin jakadancin kasashen yammacin duniya dake kasar Somaliya. Har yanzu ba a tabbatar da asalin kasashen mutanen da suka mutu a sakamakon fashewar boma-boman ba.
Kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da alhakin kai wannan hari. (Zainab)