in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Somaliya za ta yi zaben shugaban kasa a karshen Oktoba mai zuwa
2016-08-08 13:50:31 cri

Hukumar zabe mai zaman kanta a Somaliya ta wallafi jadawalin gudanar da zabe shugaban kasa a watan Oktoba mai zuwa. Shugaban hukumar zaben kasar Mista Omar Mohamed Abdulle, ya ce zaben majalisar doka za' a yi shi a ranar 25 ga watan Satumba, sannan za a nada mambobin majalisar daga ranar 24 ga watan Satumba zuwa ranar 10 ga watan Oktoba. Ya ce, za'a gudanar da zaben shugaban kasar a ranar 25 ga watan Oktoba.

Shugabannin hukumomin gwamnatin da na kafa doka da kuma na ba da shari'a na kasar sun yi alkawarin cewa, ba za su tsawaita wa'adin aikinsu ba wanda za a kammala a watan Satumba mai zuwa.

Ana sa ran cewa, zaben zai kasance zabe na farko mai adalci a kasar, wanda kowa na da cikakken hakkin jefa kuri'a nan da shekara ta 2020. (Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China