in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Al-Shabaab sun halaka mutane a kalla 6 a Somaliya
2016-08-01 09:29:37 cri
A jiya ne mayakan Al-Shabaab suka kaddamar da wani hari a hedkwatar sashen binciken manyan laifuffuka na kasar Somaliya (CID) da ke Mogadishu, babban birnin kasar, harin da ya yi sanadiyar rayukan mutane a kalla 6, kana aka kashe maharan guda 7.

Ministan tsaron kasar Somaliya Abdirizak Mohamed ya shaidawa kafofin watsa labarai cewa, 'yan bindigar sun yi yunkurin kutsa kai cikin hedkwatar binciken manyan laifuffanka ce, amma 'yan sanda suka taka musu birki.

Bayanai sun tabbatar da cewa, mayakan na Al-Shabaab sun kashe fararen hula 5, dan sanda 1 sai kuma mutane 7 daga bangaren maharan. Wani jami'in kiwon lafiya ya ce, a kalla mutane 16 ne suka jikkata kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

Tun da farko dai rundunar 'yan sandan kasar ta sanar da cewa, wasu tagwayen bama-bamai da aka dana a cikin wata mota sun fashe a kusa da mashigar hedkwatar binciken manyan laifuffuka ta kasar, daga bisani kuma sai aka ji karar harbe-harbe sun biyo baya.

Tuni dai kungiyar ta Al-Shabaab ta sanar da daukar alhakin kai harin. Shi dai wannan hari yana zuwa ne kwana guda bayan makacin wannan harin da aka kai. Ko da a makon da ya gabata ma kungiyar Al-Shabaab ta kaddamar da wani hari a kofofin shiga sansanonin tawagar MDD da na kungiyar tarayyar Afirka da ke birnin Mogadishu, hare-haren da suka haddasa mutuwar 13, kana wasu 17 kuma suka jikkata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China