in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Somaliya ya yi kiran da a karfafa tsaro a lokacin zabuka
2016-08-09 09:56:29 cri

Shugaban kasar Somaliya Hassan Cheikh Mohamud ya yi kira a ranar Litinin ga dakarun kungiyar tarayyar Afrika (AMISOM) da kuma jami'an tsaron kasar Somaliya da su kara kafafa tsaro a lokacin zabuka masu zuwa.

Hassan Cheikh Mohamud ya bayyana cewa, sojojin Somaliya da dakarun AMISOM za su aiki tare domin tabbatar da tsaron zabukan 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa wadanda za su fara a wata mai zuwa.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Somaliya ta sanar a ranar Lahadi cewa, zaben shugaban kasa na shekarar 2016 zai gudana a ranar 30 ga watan Oktoba, zaben kananan hukumomi zai gudana a ranar 24 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Oktoba, kana zaben 'yan majalisa zai gudana a ranar 25 ga watan Satumba.

Wannan zai kasance karo na farko a Somaliya, fiye da shekaru 40 da suka gabata, inda masu kafa kuri'u 14025 da suka yi rijista za su zabi shugabanni. Shugaba Mohamud ya jaddada cewa, zabukan za su kasance kamar wani babban lokaci ga kasar ta Somaliya a cikin kokarinta na ko da yaushe zuwa bisa turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Haka kuma, ya bukaci jami'an tsaro da su kasance cikin takwana, inda ya kara da cewa, kungiyar ta'addanci ta Al-Shebab za ta iya kokarin lalata zabukan da kuma hana masu zabe gudanar da 'yancinsu na demokuradiyya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China