in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kasashen gabashin Afrika ta yi tur da harin otel a babban birnin Somaliya
2016-06-27 11:08:26 cri
Hukumar inganta ayyukan gwamnati IGAD ta yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan otel din Nasa Hablod a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

A wata sanarwa da hukumar din ta gabashin Afrika ta fitar a jiya Lahadi, ta yi matukar nuna alhini game da harin wanda kungiyar Al Shabaab ta kaddamar a ranar 25 ga wannan wata a otel din Nasa Hablod, lamarin da ya haddasa mutuwar mutanen da basu ji ba basu gani ba.

IGAD ta yi Allah wadai da kakkausar murya, inda ta bayyana maharan da cewar marasa tausayin rayuwar bil adama ne.

Hukumar ta IGAD ta gabatar da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Somali da alummar kasar da kuma iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

Sannan tana fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata a sanadiyyar harin.

A cewar kakakin ma'iakatar tsaron kasar Abdikamil Mo'allim Shukri, kimanin mutane 16 ne aka tabbatar da mutuwar su ciki har da wani minsita guda, sannan sama da mutane 30 ne suka samu raunuka. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China