Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, gwamnatin Sin da kuma jama'arta suna jajantawa jama'ar kasar Faransa, kuma suna tare da jama'ar Faransa.
Kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa da kasar Faransa da sauran kasashen duniya a kokarin da ake na yaki da ta'addanci da kiyaye zaman lafiya a duniya.
A game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Jumma'a a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi Allah wadai da wannan harin ta'addanci. Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Faransa da kuma karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Marseille na kasar Faransa za su dauki matakan gaggawa domin gudanar da bincike kan batun.
Mr. Lu ya jaddada cewa, kasar Sin ita ma tana fama da kalubalen harin ta'addanci. Gwamnatin Sin za ta nace ga yaki da duk wani nau'in ta'addanci. A don haka za ta hada kai da kasar Faransa da sauran kasashen duniya wajen kare rayukan jama'a da kiyaye zaman lafiya a duniya.(Lami)