in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birtaniya ta sanya 'Turkistan Islamic party' cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda
2016-07-19 13:37:06 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Birtaniya ta sanar da sabon jerin sunayen kungiyoyin 'yan ta'adda da kasar ta tabbatar da su a kwanakin baya, inda Birtaniyar ta zayyana 'Turkistan Islamic party' da aka kafa a nan kasar Sin a matsayin daya daga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Cikin bayanin da aka gabatar tare da jerin sunayen, an ce 'Turkistan Islamic party' kungiya ce ta masu kaifin ra'ayin Islama da 'yan a-ware, wadda aka kafa ta a yammacin kasar Sin a shekarar 1989, da nufin gudanar da ayyukan da za su janyowa kasar Sin baraka a arewa maso yammacin kasar. A halin yanzu, kungiyar ta fi gudanar da ayyukanta ne a kasar Sin, da tsakiya da kuma kudancin nahiyar Asiya, da kasar Sham.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China