Kwamitin sulhu na MDD ya ba da sanarwa a jiya Litinin, inda ya yi Allah wadai da farmakan ta'addanci da aka kai a birnin Baghdad, babban birnin kasar Iraki, kana ya yi kira da a yaki da dukkan ire-iren ayyukan ta'addanci.
A cikin sanarwar, kwamitin sulhu ya nanata cewa, kowane irin aikin ta'addanci ya zama kalubale ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, dole ne a gurfanar da dukkan 'yan ta'adda da masu samar da taimako gare su a gaban kotu. A sa'i daya, kwamitin sulhu na MDD ya kalubalanci dukkan kasashen duniya da su yi hadin gwiwa tare da gwamnatocin da abin ya shafa bisa dokar duniya da ka'idojin kwamitin sulhu.
An kai farmakan ta'addanci na kunar bakin wake cikin mota sau biyu a safiyar ranar 3 ga wata, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 166, a yayin da mutane 230 suka jikkata. Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin batun.(Lami)