in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yabawa Birtaniya da ta shigar da kungiyar ETIM a cikin jerin sunayen kungiyoyin ta'addanci
2016-07-22 10:33:59 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a jiya Alhamis cewa, Sin ta nuna yabo ga kasar Birtaniya kan yadda ta shigar da kungiyar ETIM a cikin jerin sunayen kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya.

Lu Kang ya bayyana cewa, ta'addanci yana daya daga cikin abokan gaban dan Adam, kuma babu wani bambanci a matakan da kasashen duniya suke dauka na yaki da ta'addanci. Kasashen duniya sun yarda cewa, kungiyar ETIM kungiyar ta'addanci ce. Sin ta yabawa kasar Birtaniya kan yadda ta shigar da kungiyar a cikin jerin sunayen kungiyoyin ta'addanci na duniya, tare da hana mutane ko hukumomi shiga ko nuna goyon baya ga kungiyar, kana ta yi maraba ga kasashen duniya ciki har da kasar Birtaniya kan yadda suka gano matsalolin da kungiyar ETIM take haifarwa.

Lu Kang ya bayyana cewa, Sin tana son hada kai tare da sauran kasashen duniya ciki har da kasar Birtaniya wajen kara yin hadin gwiwar yaki da ta'addanci, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da tsaron lafiyar jama'a da dukiyarsu a duk duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China