Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya aika da sakon jajantawa ga takwaransa na kasar Faransa Manuel Valls kan harin ta'addanci da aka kai a bnirnin Nice, kuma ya yi Allah wadai da masu kai jari tare da nuna juyayi ga mutanen da suka mutu, daga nisani kuma, ya jajanta wa iyalan wadannan mutane.
Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, gwamnatin Sin da kuma jama'ar kasar sun nuna jajantawa ga jama'ar kasar Faransa, za ta dauki matsayi iri daya tare da jama'ar Faransa, tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Faransa da kuma sauran kasashen duniya domin yaki da ta'addanci da kiyaye zaman lafiya a duniya.(Lami)