in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijar na ziyarar aiki a shiyyar Turai
2016-06-18 12:14:45 cri
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, na birnin Berlin na kasar Jamus tun a ranar Alhamis da yamma, inda yake ziyarar aiki ta kwanaki biyu, a cewar fadar shugaban kasar Nijar a ranar Jumma'a.

Bisa jadawalin ziyararsa a Jamus, shugaba Issoufou zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Kafin kasar Jamus, shugaban Nijar ya isa Paris na kasar Faransa, inda ya kai ziyarar aiki ta kwanaki hudu daga ranar 13 zuwa 16 ga watan Yuni.

A babban birnin Faransa, Mahamadou Issoufou ya samu tattaunawa tare da manyan jami'an Faransa da suka hada da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande a ranar Talatar da ta gabata a fadar Elysee, ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da kuma ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian.

Wannan rangadi a cikin manyan biranen Turai biyu ya zo daidai da lokacin da bangaren gabashin Nijar yake fama da munanan hare haren kungiyar Boko Haram dake karuwa a lokacin baya bayan nan.

Harin baya bayan nan na ranar uku ga watan Yuni ya shafi wani sansanin jami'an tsaron Nijar na FDS dake Bosso na jihar Diffa dake kuriyar kudu maso gabashi, kusa da iyaka da Najeriya. Harin da ya halaka sojojin Nijar kusan talatin, da kuma janyo hijirar mutane fiye da dubu 50. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China