Firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya shugabanci taron ministoci karo na farko a jiya ranar 27 ga wata bayan janyewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai wato EU, inda Cameron ya bayyana cewa, yanzu gwamnatinsa na da wani muhimmin aiki, wato tabbatar da hadin kan al'ummar kasar bayan da aka jefa kuri'ar raba gardama.
Bayan taron kuma, Cameron ya furta a gaban 'yan majalisar wakilan kasar, cewar dole ne a girmama kudurin da jama'ar kasar Birtaniya suka tsayar bayan jefa kuri'ar raba gardama. Ko da yake kasar Birtaniya ta janye jikinta daga EU, amma ba za ta nisanci kasashen Turai da sauran kasashe ba. Ya kara da cewa, ministocin kasar sun amince kafa wata sabuwar hukuma domin daidaita batutuwan da ke da nasaba da janyewar kasar daga EU.
Wata sabuwar kuma, an ce, firaministar Jamus Angela Merkel, shugaban kasar Faransa François Hollande da firaministan kasar Italy Matteo Renzi sun yi ganawa a ranar 27 ga wata a birnin Berlin. Daga baya sun gabatar da wani shirin hadin gwiwa kan cewar, ya kamata kungiyar EU ta yi kwaskwarima a fannonin tsaro, tabbatar da adalci a cikin zamantakewar al'umma da kuma kyautata kwarewar matasa wajen aiki.(Kande Gao)