in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 16 sun rasu sakamakon fadowar wani babban balan-balan a Amurka
2016-07-31 16:57:35 cri
Jiya Asabar, wani babban balan-balan na masu yawon shakatawa ya fado kasa a jihar Texas ta kasar Amurka, lamarin dai ya haddasa rasuwar dukkan mutane 16 dake kan wannan babban balan-balan.

Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, hadarin ya auku ne da wajen karfe 8 saura mintoci 20 na safiyar ranar Asabar da ta wuce, wajen da lamarin ya faru yana da nisan kilomita 48 daga Austin babban birnin jihar.

Haka kuma, 'yan sandan wurin sun tabbatar da aukuwar hadarin.

A halin yanzu, ma'aikatan hukumar kula da harkokin jiragen sama ta kasar Amurka da kwamitin tsaron sufurin kasa suna binciken wannan lamari.

Bugu da kari, kwamitin tsaron sufurin kasar Amurka ya bayyana cewa, wannan shi ne hadarin babban bala-balan mafi girma da ya haddasa hasarar rayukan mutane masu yawa a tarihin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China