in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barack Obama ya ce, Amurka ba ta da masaniyar yunkurin juyin mulki a Turkiya
2016-07-23 12:58:43 cri
A jiya Jumma'a, shugaba Barack Obama na Amurka ya ce, kasarsa ba ta masaniya game da yunkurin juyin mulki a kasar Turkiyya kafin aiwatar da juyin mulkin wanda bai kai ga nasara ba. Obama ya ce, irin wannan zargi kuskure ne.

A yayin wani taron manema labaru da aka shirya tare da takwaransa Enrique Peña Nieto na kasar Mexico, wanda ke ziyarar aiki a kasar Amurka, Mr. Obama ya bayyana cewa, irin wannan jita-jita za ta kawo barazana ga 'yan Amurka wadanda suke kasar Turkiyya, kuma za ta kawo illa ga dangantakar dake kasancewa a tsakanin Amurka da Turkiyya.

Barack Obama ya nanata cewa Amurka ta yi tur da yunkurin kifar da gwamnatin Turkiyya wadda jama'a suka zaba. Amma a waje daya, ya bayyana cewa, yana fatan kada gwamnatin Turkiyya ta dauki matakan mayar da martani fiye da kima.

A sau da dama gwamnatin kasar Turkiyya ta sha zargi Fethullah Gullen, wani malamin addini dan Turkiyya wanda yanzu haka yake zaune a kasar Amurka da yin jagorancin wannan juyin mulki da bai samu nasara ba, kuma Turkiyyar ta nemi kasar Amurka da ta tisa keyar Gullen zuwa kasar Turkiyya. Game da wannan lamari, Barack Obama ya nemi kasar Turkiyya da ta gabatar da abubuwan da za su iya tabbatar da cewa Fethullah Gullen yana da hannu a wannan juyin mulki domin biyan bukatun gwamnatin kasar Turkiyya bisa doka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China