A wannan rana, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka, Peter Cook ya bayyana a cikin wata sanarwar cewa, sakamakon abkuwar juyin mulkin soja da bai yi nasara ba a Turkiya a daren ranar 15 ga wata, kawo yanzu Turkiya ta hana zirga zirgar jiragen sama a sararin samaniyarta dake karkashin kulawar sansanin Incirlik. Sojojin Amurka da na hadaddiyar kungiyar kasashen duniya suna amfani da wannan sansanin soja domin yaki da kungiyar IS dake Iraki da Syria. Yanzu Amurka tana mu'amala da Turkiya, da zummar farfado da amfani da sansanin tun da wuri. Kuma Peter Cook ya kara da cewa, sabo da ana amfani da wutar lantarki da aka samar daga cikin sansanin na Incirlik, shi ya sa karancin wutar lantarki a kasar Turkiya bai yi illa wajen cigaba da gudanar da al'amurra a wannan sansani ba.(Fatima)