in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: tsarin makamai masu linzami na Thaad da Amurka za ta jibge a Koriya ta Kudu ya wuce bukatun tsaro na zirin Koriya
2016-07-10 13:28:33 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, game da batun jibge makamai masu linzami na Thaad a kasar Koriya ta Kudu da kasar Amurka ke shiryawa, kasar Sin ta bayyana ra'ayinta na rashin jin dadi. Kasar Sin na ganin cewa, aikin jibge makamai masu linzami na Thaad ya wuce bukatun tsaro na zirin Koriya. Don haka, kowace hujja aka bayar game da batun ba ta da amfani.

Wang Yi, ya fadi haka ne yayin da yake zantawa da wakilin CRI a birnin Colombo, babban birnin kasar Sri Lanka jiyaAsabar. Wang ya kuma kara da cewa,

"Muna da dalili da kuma hakki wajen shakkar ainihin makarkashiyar wannan batun. Mun bukaci Amurka da ta dakatar da kiyaye tsaron kanta ta hanyar tada hankalunan sauran kasashe, balle ma lalata muradun tsaron sauran kasashe bisa hujjar kawo barazana ta fuska tsaro. Haka kuma muna fatan abokan kasar Koriya ta Kudu za su iya yin la'akari sosai kan cewa, ko aikin jibge tsarin Thaad zai iya ba da taimako wajen kiyaye tsaron kasarku ko a'a, ko zai iya ba da kyakkyawan tasiri wajen tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya ko a'a, ko zai iya taimakawa wajen warware batun nukiliya na zirin ko a'a. Dole ne bangarorin da abin ya shafa su yi taka tsantsan kan batun, kada su yi babban kuskure." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China