in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Turkiya ya yi kwaskwarima a tsarin sojan kasar
2016-07-31 13:14:43 cri
Jiya Asabar shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da yin kwaskwarima a tsarin sojan kasar, inda fadar shugaban kasa ce za ta shugabanci hedkwatar ba da nasiha ga rundunar sojan kasar, da kuma hukumar kula da leken asirin kasar kai tsaye.

A daren wannan ranar, shugaba Erdogan ya bayyana cewa, kasar Turkiya tana biyawa Amurka bukatunta a duk lokacin da Amurkar ta nema a maida mata masu laifi kasar, amma har zuwa yanzu, Amurkar ba ta mika mata dan kasar Turkiya Fethullah Gulen ba, kaza lika, ya ce, kasarsa za ta cigaba da neman masu daurewa "aikace-aikacen Gulen gindi" wadanda suke boye a cikin rudunonin soji, da 'yan sanda da kuma hukumar shari'a ta kasar, haka kuma, kasar za ta ci gaba da dukufa wajen yaki da 'yan ta'adda.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda suke da hannu a yunkurin wargaza tsarin siyasa a wannan kasa, da kuma kokarin kawar da masu goyon bayan "aikace-aikacen Gulen" a kasar.

A daren ranar 15 ga watan nan da muke ciki ne, aka shirya juyin mulki a kasar Turkiyya wanda bai samu nasara ba, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane 237, yayin da mutane 2191 suka jikkata. Bayan aukuwar wannan lamari, gwamnatin kasar Turkiya ta zargi dan kasarta Fethullah Gulen da shirya wannan juyin mulki, wanda a halin yanzu yake zaune a kasar Amurka, kasar Turkiya ta bukaci Amurka da ta mai da shi kasarta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China