Bisa sanarwar da aka bayar a shafin internet na shugaban kasar Rasha a ranar 27 ga wata, Erdoğan ya bayyana a cikin wasikar cewa, yana son yin hadin gwiwa tare da kasar Rasha wajen daidaita batun harbi jirin saman yaki na Rasha, tare da nuna jajantawa ga iyalan mai tukin jirgin saman da ya mutu a sakamakon harin.
Kana Erdoğan ya bayyana cewa, kasar Rasha abokiya ce ta kasar Turkiya, kasarsa ba ta da niyyar harbi jirgin saman Rasha da gangan. Kasar Turkiya tana son mayar da dangantakar dake tsakaninta da Rasha, tare da yin hadin gwiwa da juna wajen warware rikici a yankin, da yaki da ta'addanci tare.
Kakakin fadar shugaban kasar Turkiya Ibrahim Kalin ya tabbatar a ranar 27 ga wata cewa, Erdoğan ya mika wasikar neman gafarar ga shugaban kasar Rasha Putin, kana ya bayyana cewa bangarorin biyu sun cimma daidaito kan daukar matakai don mayar da dangantakar dake tsakaninsu cikin hanzari. (Zainab)