Haka kuma, sanarwar ta ce, cikin wadannan mutane 41 da suka rasu, akwai mutane 12 da suka zo daga ketare, ciki har da 'yan kasashen Saudiyya da Iran da Ukraine da sauransu.
Firaministan kasar Turkiya Bina Le Yıldırım ya bayyana a safiyar jiya Laraba cewa, akwai alamun da ke nuna cewa, kungiyar IS ce ta kai wannan hari, amma har yanzu, ana ci gaba da bincike don gano 'yan ta'addan da suka kai harin.
Gwamnatin kasar Turkiya ta kafa kwamitin musamman domin fuskantar harkokin gaggawa bayan aukuwar lamarin, rundunar 'yan sandan kasar ta kuma rufe filin saukar jiragen sama na Ataturk, da kuma dakatar da dukkan jiragen sama dake shiga ko fita daga filin. (Maryam)