Firaministan kasar Turkiya Binali Yildirim ya bayar da sanarwa a safiyar yau Laraba cewa, kungiyar IS ce ta tayar da jerin boma-boman.
A jiya da dare shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ya bayar da sanarwa a rubuce, inda da babbar murya ya la'anci wannan harin na ta'addanci, ya kuma kalubalanci kasashen yamma da su dauki kwararan matakai wajen yaki da ta'addanci.
Sanarwar ta kuma nuna cewa, an kaddamar da wannan harin ta'addanci ne a watan azumi, wannan ya nuna cewa, 'yan ta'adda sun mayar da fararen hula a matsayin abubuwan da suka kai hari, da nufin lalata Turkiya ta hanyar zubar da jini.
A wannan rana kuma, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya la'anci harin ta'addanci da aka kai a filin jirgin saman na Atatürk, ya kuma jaddada cewa. Ya kamata kasashen duniya su kara kokari don yaki da ta'addanci. (Bilkisu)