A wannan rana, Sergei Lavrov ya gana da Mevlut Çavusoglu a birnin Sochi na Rasha, wanda ya isa can domin halartar taron kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki na yankin Black Sea. Bayan ganawarsu, Sergei Lavrov ya bayyana wa kafofin yada labarai cewa, kasashen biyu sun taba kafa wani rukunin yaki da ta'addanci cikin hadin gwiwa, amma sabo da Turkiya ta harbe jirgin saman yakin Rasha, lamarin ya janyo dakatar da aikin wannan rukuni a cikin watanni 7 da suka wuce. Amma sabo da aikin yaki da ta'addanci cikin hadin gwiwa tsakanin Rasha da Turkiya na da muhimmanci sosai, shi ya sa bangarorin biyu sun dora niyyar farfado da aikin wannan rukuni, tare da kafa hanyar mu'amala tsakanin rundunonin sojan kasashen biyu.
Dadin dadawa, Sergei Lavrov ya kara da cewa, bisa shawarar da shugabannin kasar Rasha suka yanke, hukumomin da abin ya shafa na kasashen biyu za su yi shawarwari kan yadda za su kyautata dangantaka tsakaninsu nan ba da dadewa ba.
A ranar 29 ga watan Yuni, shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdoğan ya buga waya ga takwaransa na Rasha Vladimir Putin, inda suka jaddada muhimmancin daukar matakan kyautata dangantakar kasashen biyu da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kuma sun yi alkawarin yaki da ta'addanci tare. Wannan ne karo na farko da shugabannin kasashen biyu suka tuntubi juna ta wayar tarho bayan tsanantar dangantaka tsakaninsu dalilin harbe jirgin saman yaki na Rasha da Turkiya ta yi a cikin watan Nuwamban shekarar bara. Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya shelanta a wannan rana cewa, shi zai gana da shugaba Vładimir Putin a gun taron koli na G20 da za a shirya a watan Satumban bana a birnin Hangzhou na Sin.(Fatima)