A jiya ne firaministan kasar Turkiya kuma shugaban jam'iyyar AKP ta kasar Ahmet Davutoglu ya sanar da cewa, ya tsaida kudurin yin murabus daga mukamin shugaban jam'iyyar AKP da kuma firaministan kasar. Jam'iyyar AKP za ta gudanar da taron musamman a ranar 22 ga wannan wata don zabar sabon shugaban jam'iyyar.
Manazarta na ganin cewa, Davutoglu bai mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin da shugaban kasar Tayyip Erdogan ya gabatar yadda ya kamata ba, lamarin da ya haifar da rashin jituwa a tsakaninsu. (Zainab)