Wang Yi ya bayyana cewa, bisa wannan taro na masu shiga tsakani da za a gudanar, Sin na fatan bayyana alama a fili ga duniya cewa, ko da yake ana fuskantar matsalar rashin samun ci gaban tattalin arziki a duniya, duk da hakan Sin za ta cika alkawarin da ta dauka. Kaza lika ana cikin yanayi mai kyau game da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma za a sami makoma mai kyau a wannan fanni.
A nasu bangare, ministocin kasashen Afirkan sun bayyana cewa, kasashen nahiyar za su yi amfani da wannan zarafi, wajen tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Johannesburg, domin gudanar da shawarwari tare da kasar Sin kan batun hadin gwiwa, da neman samun ci gaba tare, da kara hada kai waje guda, ta yadda za su kara amincewa da nuna wa juna goyon baya, kan batutuwan da suka shafi babbar moriyar juna, da ma sauran harkokin da suka fi jawo hankulan bangarorin biyu.(Fatima)