in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron kawar da talauci da samun bunkasuwa na FOCAC
2015-12-09 10:57:23 cri

An bude taron kawar da talauci da samun bunkasuwa, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a jiya Talata.

Taken taron shi ne "hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka game da kawar da talauci, da samun bunkasuwa bayan shekarar 2015". Kaza lika taron na da manufar karfafa mu'amala tsakanin kasashen duniya a fannin fasahohin kawar da talauci, da neman hanya mafi dacewa wajen sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka game da yaki da talauci.

Ofishin kula da harkokin yaki da talauci da raya kasa na majalissar gudanarwar kasar Sin, da ma'aikatar kula da harkokin bunkasuwar kauyuka da kwaskwarima kan yankuna ta kasar Afirka ta Kudu ne suka karbi bakuncin gudanar da taron, inda jami'an gwamnatoci, da masana, da wakilan kamfanoni da kafofin watsa labaru daga kasashen Sin da Afirka kamar Afirka ta Kudu, da Ghana, da Nijeriya, da Senegal da sauransu, wadanda yawansu ya kai fiye da 150 ne suka halarci taron na kwanaki biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China