Lu Kang ya ce, masu shiga tsakani kan sakamakon da aka cimma a gun taron kolin Johannesburg na kasashen Afirka 52, da jakadun kasashen Afirka a Sin, da wakilan kamfanonin kwamitin kula da ci gaban dandalin FOCAC da sauransu za su halarci wannan taro. Dadin dadawa, za a kira taron shawarwari tsakanin shugabannin hukumomin hada hadar kudi na Sin da mahalarta taron daga kasashen Afirka, da taron musayar ra'ayi kan hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya tsakanin bagarorin biyu, da bikin rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa da sauransu.
Lu Kang ya bayyana cewa, makasudin shirya wannan taro shi ne musayar ra'ayi kan sakamakon da aka samu ta hanyar yin hadin gwiwa, da yin mu'amala kan yin hadin gwiwa, da kara sa kaimi ga tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron kolin Johannesburg, ta yadda za a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka domin samun ci gaba tare.(Fatima)