Kakakin ofishin jakadancin Sin a kasar ta Afirka ta Kudu Hu Zhangliang, ya ce, kasarsa na da aniyar aiwatar da daukacin kudurorin da aka cimma, a yayin taron dandalin tattaunawar hadin kan na Sin da Afirka wato FOCAC.
Hu Zhangliang, wanda ya bayyana hakan ga mahalarta wani taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki game da taron na FOCAC a birnin Pretoria, ya ce Sin za ta cika alkawuran ta, duk kuwa da mawuyacin halin tattalin arziki da ake fuskanta a yanzu haka.
Ya ce taron na birnin Johannesburg da ya gabata a watan Disamba, ya dada karfafa irin kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, kuma dukkanin kudurorin da aka cimma, na tabbatar da burin da aka sanya gaba, na cimma moriyar juna tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka.
Daga nan sai Hu ya sake jaddada bukatar da ke akwai, ta kafa ginshikin mai karfi, wanda zai tallafawa burin da aka sanya gaba, na fadada dangantaka tsakanin Sin da Afirka, duba da cewa tuni sassan biyu suka nuna burin su na daga matsayin alakar su zuwa mataki na gaba.(Saminu Alhassan)