in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da taron masu shiga tsakani kan sakamakon da aka samu a taron koli na Johannesburg na FOCAC
2016-07-22 15:44:53 cri

A ranar 29 ga wata ne za a gudanar da taron masu shiga tsakani kan yadda ake tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka (FOCAC) da aka gudanar a birnin Johannesburg a birnin Beijing.

Shugaban kwamitin kula da ayyukan da suka biyo bayan dandalin tattaunawar FOCAC na Sin, kana mataimakin ministan harkokin wajen Sin, Zhang Ming ya bayyana yau Jumma'a 22 ga wata a Beijing cewa, bisa kokarin da Sin da kasashen Afirka suke yi tare, an samu ci gaba game da wasu sakamakon da aka cimma a gun taron kolin, duk da wasu matsaloli da aka fuskanta, wannan ya sa za a daidaita wadannan matsaloli a gun taron masu shiga tsakani da za a yi a ranar 29 ga wata, ta yadda za a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka da tabbatar da sakamakon taron kolin.

Tabbatar da sakamakon taron kolin ba ma kawai zai sa kaimi ga samun ci gaba tsakanin Sin da kasashen Afirka ba, har ma zai samar da yanayi mai kyau ga kasashen duniya wajen zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kasashen Afirka. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, wasu kafofin yada labarai sun yi ta yada jita-jita cewa, Sin ta karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka domin yin takara da kasashen yammacin duniya. Game da wannan batu, Zhang Ming ya ce, kasashen Afirka da jama'arsu na da cikakken 'yancin zaben abokan hadin gwiwa da hanyar hadin gwiwa, a saboda haka wannan batu ba shi da wata alaka da yin takara.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China