Kasar Sin a shirye take kana kofarta a bude take wajen raba kwarewarta tare na nahiyar Afrika a fannin samun bunkasuwa, in ji mista Jose Mario Vaz a gaban manema labarai bayan ya koma kasarsa a ranar Laraba. Shugaban Guinea-Bissau ya jaddada cewa, dangantakar Sin da Afrika, dangantaka ce mai muhimmanci bisa ta manyan tsare tsare,wadda ke iya jurewa kalubale na rashin cigaba. A cewar shugaba Jose Mario Vaz, hadin kai a tsakanin Afirka da kasar Sin zai dore, wato za a cigaba da samar da karin moriyar juna. (Maman Ada)